1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa tsakanin Guterres da Putin

Suleiman Babayo ABT
April 26, 2022

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya zai gana da shugaban kasar Rasha kan samun mafita a yakin Ukraine daga bisani zai garzaya zuwa Ukraine domin ganawa da shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/4AR3r
UN-Generalsekretär António Guterres
Hoto: Bruce Cotler/ZUMA /picture alliance

A wannan Talata aka tsara Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres zai gana da Shugaba Vladimir Putin na Rasha a birnin Moscow fadar gwamnatin kasar domin tattauna hanyoyin diflomasiyya na kawo karshen yakin da aka kwashe watanni biyu ana fafatawa bayan Rasha ta kaddamar da kutse a kan Ukraine.

Tattaunawar ta fadar Kremlin za ta mayar da hankali kan rawar diflomasiyya da Majalisar Dinkin Duniya bisa warware yakin da ke faruwa a Ukraine, gami da samar da hanyoyin da za a samar da mafita ga fararen hula da suke wuraren yaki ya yi zafi.

Kana babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai shekaru 74 da haihuwa zai gana da Sergei Lavrov ministan harkokin wajen kasar ta Rasha. Tun farko dai Babban jami'in MDD ya gana da Shugaba Recep Erdogan na Turkiyya a kan hanyar tafiya kasashen da ke samun sabani da juna.

Daga Rasha, sai kuma António Guterres babban jami'in na MDD ya zarce zuwa kasashen Poland da Ukraine, inda ake sa ran zai gana da Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar ta Ukraine ranar Alhamis mai zuwa.