1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaushe matsalolin za su kare a Iraki?

Mahmud Yaya Azare LMJ
March 2, 2023

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya na ziyara a Iraki, a daidai lokacin da al'ummar kasar ke zanga-zangar adawa da sauya kundin tsarin mulki.

https://p.dw.com/p/4OBNi
Iraki | Bagadaza | Antonio Guterres | Fuad Hussein
Antonio Guterres tare da ministan harkokin kasashen wajen Iraki Fuad HusseinHoto: Murtadha Al-Sudani/AA/picture alliance

Ziyarar sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniyar António Guterres na zaman ta farko cikin shekaru shida, tun bayan shelanta kawo kungiyar 'yan ta'addan IS. Ziyarar tasa kuma na zuwa ne a daidai lokacin da ake cika shekaru 20 da kawar da mulkin Shugaban Saddam Hussein da sojojin Amurka suka tunbuke shi bayan da kaddamar da yaki a kasar. Yayin ziyarar ta Guterres dai, bayan ganawa da mahukuntan Irakin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam da na masu rajin kafa dimukuradiyya, ya ce ya ziyarci kasar ne domin karfafa guiwa ga al'ummarta da ke murmurewa daga ta'annutin kungiyar IS shekaru biyar din da suka gabata. Bayan nuna goyan baya ga al'ummar ta Iraki da jinjina musu da ya yi kan nasarar tunkarar tarin kalubalen tsaro da na zamantakewa da yunkurin tarwatsa kasar da suka yi, Guterres ya jaddadawa shugabanin na Iraki muhimmancin hadin kai da hakurin zama da juna domin sake gina kasar da samun ci-gaba.

Ya kuma yi kira ga 'yan siyasa da su mutunta yarjejeniyar fahimtar juna da suka cimma tsakaninsu, domin ganin an gudanar da zaben da zai samar da kwanciyar hankali da ci-gaban kasa. Ba ya ga haka kuma, ya yi bukaci da a samar da wani tsarin afuwa na gama-gari da zai bai wa dubban Irakawan da ke samun mafakar siyasa a ketare damar komawa  kasarsu su kuma gina ta. A nasa bangaren firaministan kasar Mohammed Shia al-Sudani wanda ya yi godiya ga sakataren na Majalisar ta Dinkin Duniya a madadin al'ummar Iraki kan irin goyan bayan da yake ba su, ya kara da bayyana masa irin kokarin da gwamnatinsa ke yi na ganin an tabbatar da zaman lafiya da tsaro ba a kasar ta Iraki kadai ba harma da yankin baki daya. Kasar Iraki da ke da dimbin arzikin man fetur baya ga kudin ajiya a asusunta da ya kai dala biliyan 100 dai, na fama da matsalolin tsaro da cin-hanci da rashawa sakamakon kabilanci da bangaranci gami da tsoma bakin kasashen ketaren. Wannan lamari dai ya sanya matasan kasar da ke kishirwar samun sauyi, gudanar da tarin zanga-zangar da ake fatan 'yan siyasar kasar za su shawo kanta ta hanyar yi wa tufkar hanci.