1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres: Mu taimaki Nijar yakar ta'addanci

Mouhamadou Awal Balarabe
May 2, 2022

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci kasashen duniya su taimaka wa sojojin Nijar wajen yaki da kungiyoyin jihadi da ke kai hari a kasar da ma wasu kasashe makwabta.

https://p.dw.com/p/4Ak1N
UN-Generalsekretär António Guterres
Hoto: Bruce Cotler/ZUMA /picture alliance

A yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum a birni Niamey, Antonio Guterres ya ce zai yi iya kokarinsa wajen ganin sojojin Nijar su samu horo da ya dace da kuma kayan aiki. Ya kara da cewa, Nijar ba za ta iya fuskantar wannan kalubalen tsaro ita kadai ba.

A nasa bangaren shugaba Bazoum na Nijar ya bayyana cewa ya tattauna da Antonio Guterres kan sabon tsarin hadin gwiwa tsakanin Nijar da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kawayenta wajen yaki da ‘yan ta’adda. A cewarsa dai, 'yan ta'adda sun sauya kamun ludayinsu, saboda haka akwai bukatar sabunta yadda ake a tinkari matsalar  ta'adda.

Dama a yaki da ayyukan ta'addanci, Nijar na samun goyon bayan wasu kasashen yammacin duniya da suka hada da Faransa da Amirka wadanda ke da sansanonin soji a Yamai da yankin Agadez da ke arewacin kasar.