1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guterres: Duniya na cikin tsaka mai wuya

Abdullahi Tanko Bala
January 18, 2023

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce tarin matsaloli da suka yi wa duniya dabaibayi da suka hada da sauyin yanayi da yakin Rasha da Ukraine sun jefa duniyar cikin halin tsaka mai wuya.

https://p.dw.com/p/4MO14
Davos WEF Rede Guterres
Hoto: Fabrice Coffrini/AFP

Guterres wanda ya gabatar da jawabi a rana ta biyu na babban taron tattalin arzikin duniya a Davos ya jaddada kalubalen da duniyar ke fuskanta na sauyin yanayi yana mai cewa alkawarin da kasashe suka dauka na rage dumamar yanayi da maki daya da rabi a ma'aunin Celcius na nema ya gagari kundila.

"Ya ce muna wasa da bala'in sauyin yanayi. A kowane mako ana samun mummunan labari na sauyin yanayi. Gurbataccen hayaki na karuwa a sararin samaniya fiye da yadda ba a tsammani yayin da kudirin kasaashen duniya na takaita dumamar yanayin da maki daya da rabi a ma'aunin celcius yake neman zama almara. Idan ba dauki kwakkwaran mataki ba za mu doshi karuwar zafin da maki biyu da digo takwas a ma'aunin Celcius".

.