Guterres: Afirka na taimakawa mabukatu | Labarai | DW | 30.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guterres: Afirka na taimakawa mabukatu

Babban sakatare Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadan rufe kan iyakokinsu da wasu kasashe da ke kiran kansu masu cigaba na duniya ke yi, a dai dai lokacin karuwar mabukatu.

Wannan dai na mai zama matarni ga furucin shugaban Amurka Donald Trump na haramtawa wasu kasashe da da akasarinsu musulmi ne izinin shiga kasar.

Sabon jagoran na MDD wanda ke magana a yayin kaddamar ta taron kungiyar gamayyar Afirka a birnin Addis Ababa na Ethiopia, ya yabawa rawa da kasashen Afirka ke takawa wajen tausayawa 'yan gudun hijira duk da yawan al'umma da nahiyar ke da shi.

" Iyakokin kasashen Afirka na ci-gaba da kasancewa a bude ga mabukatu, a daidai lokacin da wasu da ke kiran kansu masu cigaba ke garkame kofofinsu"

Taron kungiyar ta AU na 28 dai na mai zama irinsa na farko tun bayan hawan Trump karagar mulki, kuma tuni aka fara jin radadin shugabancinsa a nahiyar ta Afirka. Taron a hannu guda zai fayyace matsayin kasar Morokko a kungiyar, shekaru 33 bayan ficewarta.