Gurfanar da Morsi a gaban kuliya | Labarai | DW | 02.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gurfanar da Morsi a gaban kuliya

Tsohon shugaban Masar zai gurfana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasar bisa zargin kisan masu bore.

Babban mai shigar da kara na gwamnatin Masar, ya mika shari'ar da za a yi wa hambararren shugaban Masar Mohammed Morsi ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasar. Morsi dai zai fuskanci tuhumar da ta shafi ingiza magoya bayan kungiyar 'yan uwa Musulmi wajen kissan a kalla masu bore 10 daga bangaren 'yan adawar kasar a cikin watan Disamban bara. Shugaba Morsi, wanda ke zama zababben shugaban Masar na farko ta hanyar dimokradiyya, sojoji ne suka kifar da gwamnatinsa ta hanyar juyin mulki cikin watan Yuli, bayan da dubun dubatan masu zanga-zanga sun yi kira ga tsigeshi daga mulkin.

Dama kuma a watan jiya ne, kotu ta sallami tsohon shugaban mulkin kama karya na Masar Hosni Mubarak daga gidan yari, bayan wankeshi daga zarge-zargen da suka shafi cin hanci da rashawa. A dai shekara ta 2011 ne, juyin juya halin kasar Masar, ya janyo kifar da gwamnatin shugaba Mubarak, wanda ya share fagen zaben shugaba Morsi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal