1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iyalan Gupta da siyasar Afirka ta Kudu

Abdul-raheem Hassan
February 15, 2019

Hukumar 'yan sandan kasar ta janye sammacin kama shahararren dan kasuwa kuma aminin tsohon shugaban kasar Jacob Zuma wato Ajay Gupta ba tare da bayyana dalili ba.

https://p.dw.com/p/3DTxs
Südafrika Polizei durchsucht Anwesen von Präsident Zumas Günstlingen
Hoto: Reuters/J. Oatway

Babu dai cikakkun bayanai kan dalilan soke sammacin kama fitaccen dan kasuwar da ake zargi da cin hanci da rashawa, amma hukumar 'yan sandan ta ce za ta iya sabunta sammacin. Lauyan da ke kare Gupta da iyalansa a kotun dai bai yi martani kan matakin hukumar 'yan sandan ba.

An dai jima ana zargin iyalan Gupta da laifukan cin hanci da neman yin sama da fadi da dukiyar kasar ta Afirka ta Kudu ta hanyar amfani da ikon tsohon shugaban kasar Jacob Zuma da ake cewa akwai alaka ta abota a tsakaninsu, sai dai Gupta ya sha karyata duk wani zargi na rashawa tare da nesanta kansa da duk wata dangantaka da Zuma.