Guna-guni kan rufe iyakokin Najeriya | Zamantakewa | DW | 08.10.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

‘Yan Niger Delta sun koka da rufe iyakar Najeriya

Guna-guni kan rufe iyakokin Najeriya

Jama’a musamman a yankin Niger Delta dake kudu maso gabashi Najeriya sun koka cewar matakin rufe iyakokin ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi.

A ranar 19 ga watan Augusta ne gwamnatin Najeriya ta bada umarnin rufe iyakokin da ke tsakaninta da makwabtan kasashe kamar Niger da Kwatano domin dakile shigo da kayayyaki cikin kasar ta barauniyar hanya. Rufe iyakokin dai ga dukkanin alamu ya haifar da babbar damuwa ga makwabtan kasashen, dama kuma wasu alummar Najeriyar su na ta kokawa kan hakan, a bisa dalilin matakin ya haifar da hauhawan farashin kayayyaki.

A kudancin Najeriya dai, alamarin rufe iyakokin ya haifar da damuwa kan hauhawar farashin na kayayyakin masarufi a cewar Mr Bemene Tanem wani dan yankin Niger Delta.

“Yace a gaskiya matakin rufe iyakokin na haifar mana da wahala matuka kuma matakin ya bai wa marasa kishin kasa amfani da damar wajen tsawwala farashin kayayyakin masarufi “.

Grenze Nigeria Benin

Kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Benin

Kayayyakin masarufin na yau da kullum da jamaa suka fi damuwa a kai sun hada da shinkafa da kifi da dai sauransu .

Mallam Baffa Ibrahim, dan kasuwar hada-hadar kayayyakin abinci ne a birnin Fatakwal ya bayyana yadda jama‘a ke kukan rufe iyakokin.

“Yace yanzu Jama‘a sun rungumi cimaka ta gida sosai maimakon ta kasashen waje“.

Yayin da wasu Jama‘a ke kokawa kan rufe iyakokin masana harkokin tattalin arziki na nuna cewar matakin zai taimaka matuka wajen tallafar tattalin arzikin Najeriyar,

Hukumar Kwastam dai ta sanar cewar tun bayan rufe iyakokin kudaden shiga da take tattarawa a kullum sun karu. Jamian hukumar Kwastam din ta hada karfi da Jamian hukumar shige da fice wato Immigration, da yan sanda da Soji, don tsananta aikin tabbatar da cewar iyakokin Najeriyar sun ci gaba da kasancewar a rufe ruf don amfanin kasar da al‘umarta.

 

Sauti da bidiyo akan labarin