Gumurzu a gabacin ƙasar Tchad | Labarai | DW | 09.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gumurzu a gabacin ƙasar Tchad

A gabacin ƙasar Tchad, a na ci gabada ɓarin wuta, tsakanin dakarun gwamnati da yan tawaye.

A wata sanarwar da ta hiddo a yau litinin, rundunar gwamnati ta bayyana hurgaɗar ayarin wasu yan tawaye cikin motoci fiye da 200, da su ka kusto daga ƙasar Sudan.

Kakakin gwamnatin ƙasar Tchad, Hurmaji Musa Dangor, ya bukaci ƙasashen dunia, su hito ƙarara, su yi Allah wadai ga kasar Sudan, a game da abinda ya kira hari na barkatai da ta kaiwa ƙasar Tchad.

Kakakin ci gaba da cewa, ya zuwa yanzu, ba a tantance yawan mutanen da su ka rasa rayuka daga ɓangarorin 2, saidai rundunar gwamatin ta rugurguza mitoci kussan 40 na yan tawayen