Guinea Conakry za ta yi zabe mai cike da rudani | Siyasa | DW | 20.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Rashin tabbas a siyasar Guinea

Guinea Conakry za ta yi zabe mai cike da rudani

A ranar Lahadin da ke tafe ne 'yan kasar Guinea Conakry za su gudanar da tagwayen zabuka da suka hada da na 'yan majalisun dokoki da zaben raba gardama na wani sabon kundin tsarin mulki.

A yanzu dai za a iya cewa a cikin wani yanayi ne mai cike da sarkakiya 'yan kasar ta Guinea Conakry za su halarci tagwayen zabukan. Ko baya ga batun 'yan majalisun dokoki, zaben na ranar 22 ga watan Maris zai ba kasar damar samun wani sabon kundin tsarin mulki da ke ciki da kace-nace. Kazalika  'yan kasar ta Guniea Conakry za su isa a runfunan zabe ne a daidai lokacin da duniya ke cikin wani tasko na annobar cutar Corona inda aka samu yaduwar cutar daga wasu 'yan kasar dadama.

Sai dai ta wannan dalilin ne na cutar Corona, Shugaba Alpha Conde ya dage ziyarar tawagar shugabannin kasashen yammacin Afirka na CEDEAO ko ECOWAS.

A cewar wani marubuci dan kasar ta Guniea Conakry Tierno Menenembo, yunkurin na karfin tuwo da shugaba Conde ke son yi na iya barin baya da kura.

" ba zai karbi bakuncin kungiyar CEDEAO ko ECOWAS ba saboda Corornavirus amma kuma ga shi za a yi zaben duk da wannan yanayi, ga alama dai shugaban na shirye ne domin tarbo aradu da ka. Idan ma za a yi zubar da jini ne a kasar wannan na nuni da cewar hakan bai dame shi ba, wautar da sojoji ke yi kowa yasan da ita a kasar nan domin mutanen da ke yi wa mata fyade da rana tsaka shirye suke duk abin da suka ga dama su yi, mu mun zuba ido kawai." inji Menenembo

Sai dai duk da wannan fargaba gwamnati a na ta bangare ta tabbatar da cewa komai ya kankama domin ganin an gudanar da zaben a cikin koshin lafiya. Papa Koly Kourouma ministan gwamnatin ne da kuma ke yakin gangamin zabe.

" Gwamnati ce ke da hurumin kare 'yan kasa da dukiyoyinsu kana kuma ina tsammanin an dauki kwararan matakai domin kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu ta yadda kawai zai je yayi zabensa ba tare da tsangwama ba.  Wasu daga cikin matakan da ak adauka sune na ganin an hana mutane yin cincirindo a runfunan zabe kana kuma jami'an tsaro za su kiyaye jama'a domin tabbatar musu da tsaro." inji Koly

Ga bangaren gwamnatin kasar batun dage zaben bai ma taso ba, haka batun saka jam'iyyun adawa don damawa da su a cikin zaben ya zama zancen 'yan matan-amarya.

Gwamnatin kasar ta kara albashin sojojinta da kaso 20 cikin dari, hakan kuma kamfanonin sadarwa sun bayyana aniyarsu ta datse layukan intanet a fadin kasar daga 21 zuwa 22 ga watan Maris har ma da kiran talho daga kasashen ketare. Makarantu kuma za su kasance a rufe har 24 ga wannan wata na Maris.

Duk a cikin wannan yanayin ne hadin gwiwar kungiyoyi da jam'iyyun yan adawa suka kira wani gangami a ranar asabar da zimmar hana Shugaba Conde gudanar da zaben na ranar Lahadi.

Sauti da bidiyo akan labarin