Guinea Conakry: ′yan takara 8 a zaben shugaban kasa | Labarai | DW | 02.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guinea Conakry: 'yan takara 8 a zaben shugaban kasa

Kotun tsarin milkin kasar ta bayyana sunayen 'yan takara takwas da za su papata a zaben shugaban kasa na 11 ga watan Oktoba mai zuwa.

A Guinea Conakry kotun tsarin milkin kasar ta bayyana jerin sunayen 'yan takara takwas da za su papata a zaben shugaban kasa da kasar za ta shirya ran11ga watan Oktoba mai zuwa. 'Yan takarar sun hada da shugaban kasar mai ci Alpha Conde da kuma da madugun 'yan adawa Cellou Dalein Diallo na jam'iyyar UFDG da kuma Marie Madeleine Dioubate ta jam'iyyar PEG.

Sai dai kotun ta yi watsi da takarar tsohon shugaban milkin rukon kwaryar sojan kasar Musa Dadis Camara wanda ke zaman gudun hijira a kasar Burkina Faso da ya bukaci shiga a papata da shi a karkashin inwar sabuwar jam'iyyarsa da ya kafa ta FPDD.

Sai dai yanzu haka ana ci gaba da samun sabani tsakanin bangarorin siyasar kasar a kan batun hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar da a kan girgam din zabe dama a kan batun zaben kananan hukumomi wanda gwamnatin kasar da dage shi har zuwa bayan na shugaban kasa.