Guinea Conakry: Kira ga Shugaba Condé | Siyasa | DW | 04.09.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Guinea Conakry: Kira ga Shugaba Condé

Bangarori dabam-dabam a kasar Guinea Conakry musamman ma matasa, na ci gaba da kira ga Shugaba Alpha Condé mai shekaru 82, da ya jingine yunkurinsa na tazarce.

Guinea Präsident Alpha Conde (Getty Images/AFP/C. Binani)

Shugaba Alpha Conde na Guinea Conakry

Bangarorin dai sun bukaci Shugaba Alpha Condé da ya kyale matasa sababin jini su dauki ragamar ikon kasar, a daidai lokacin da yake ikrarin cewa karin   nwa'adi na ukua mulkin nasa, zai ta'allaka ne ga mata da matasa. A can baya dai Shugaba Conde ya taba bayyana cewa a ganinsa yawan shekaru ba ya taba zama wata illa ga harkokin tafiyar da mulki da ma wakiltar matasa.

A shekarar 2017 yayin wata hirarsa da tashar DW game da yiwuwar ya sake tsayawa takara a wa'adi na uku, Shugaba Condé ya bayyana batun da wani rudani kawai, kana kuma da yake tsokaci game da batun adadin shekarun kasancewa a kan madafan iko, Conde ya yi wani jirwaye ne mai kamar wanka: "Batun adadin shekaru don jagorantar kasa, duk wannan wani zance ne na dabam, domin kuwa da akwai shugabannin da suke da yawan shekaru kuma suke tafiyar da sha'anin mulkinsu yadda ya kamata ba tare da wata tangarda ba, ko da yake da akwai wasu masu gudanar da mummunan jagoranci, lamarin da ke harzuka matasa har su dinga hankoron neman sauyi a kasashensu."

Guinea Wahlkampf 2015 (DW/B. Barry)

Zabne Guinea Conakry a shekara ta 2015

Shekaru uku bayan wannan hira, a yanzu rukunin mata 'ya'yan jam'iyyar RPG mai mulki da hadin gwiwa da takwarorinsu na gungun jam'iyyun da ke mulki, sun tattara kudi domin sayen tikitin tsayawar shugaban takara a zaben watan Oktoban da ke tafe. A yanzu dai za a iya cewa shugaba Alpha Condé ba ya fargabar tunkarar duk wani shamaki na ya tufka ko kuma ya warware. Matan dai na cewa su ne ke kan gaba wajen tabbatar da muradun duk wani dantakara na zaben shugaban kasar Gunie Konakry.

Sai dai wannan fata na cin karo da muradun wasu matasa, musamman ma masu fama da zaman kashe wando tun bayan da Shugaba Conde ya dare kan madafan iko a shekarar 2010. A ranar Alhamis din da tagaba ne Shugaba Alpha Conde ya ajiye takardar bukatar takararsa a gaban kotun tsarin mulki, a daidai lokacin da zanga-zangar adawa da tazarcen ke ci gaba da kamari a yankunan kasar kusan mako guda ke nan, tun bayan da shugaban ya tabbatar da cewa zai sake tsayawa takarar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin