1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasuwar Guido Westerwelle na Jamus

Ondruskova, Iveta / Mohammad Nasiru Awal/ LMJMarch 20, 2016

A wannan Jumma'ar tsohon ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya rigamu gidan gaskiya yana da shekaru 54 a duniya.

https://p.dw.com/p/1IG6P
Guido Westerwelle
Hoto: DW/M.Müller

Westerwelle da ya shafe tsawon shekaru 10 yana jagorantar jam'iyyar FDP ta masu sassaucin ra'ayi, ya kuma rike mukamin ministan harkokin wajen Jamus daga shekara ta 2009 zuwa 2013, ya rasu ne sakamakon cutar kansar jini wato Leukemie da ya yi fama da ita.

Taka rawa a siyasa da harkokin diplomasiyya

Guido Westerwelle ke nan lokacin da yake sanar da ajiye mukaminsa a matsayin shugaban FDP, inda ya ayyana ci gaba da rike mukaminsa na ministan harkokin wajen Jamus, a wani taron manema labarai a birnin Berlin, ranar 3 ga watan Afrilun 2011 inda ya ce:

"Bayan shekaru 10 a matsayin shugaban jam'iyya ba zan sake tsayawa takarar neman shugabancin jam'iyya a babban taronta na watan mayu ba. Wannan shawara ce mai wahala da na yanke. Amma ya zama wajibi in ja baya in ba wa sabbin jini wuri don jagoranci jam'iyya."

Guido Westerwelle, tare da minstan harkokin kasashen Jamus mai ci Frank-Walter Steinmeier
Guido Westerwelle, tare da minstan harkokin kasashen Jamus mai ci Frank-Walter SteinmeierHoto: Getty Image/AFP/J. MacDougall

Tun yana karami yake da sha'awar siyasa, ya shiga jam'iyyar FDP tun yana dan shekaru 19, ya kuma kasance daya daga cikin wadanda suka kafa bangaren matasa na jam'iyyar. A gefe guda ya yi ilimin fannin shari'a, bayan ya samu digirin digir-gir a matsayin lauya. Yana da shekaru 33 ya zama babban sakataren jam'iyya, sannan ya rike mukamin shugaban jam'iyya na tarayya yana da shekaru 39, inda ya zamona farko da aka taba samu a wancan lokaci.

Janyo hankalin matasa cikin siyasa

A tsawon shekaru 10 na jagorancin jam'iyyar ta FDP, burinsa shi ne ya jawo hankalin matasa zuwa ga jam'iyyar. Bayan zaben majalisar dokokin Bundestag a shekara ta 2009, jam'iyyar ta samu yawan kuri'u da ke zama na tarihi, wato sama da kaso 14 cikin 100, abin da ya bata damar kulla kawance da jam'iyyar CDU tare da kafa gwamnati karkashin shugabar gwamnati Angela Merkel. A nan dai kusan burin Guido Westerwelle ya cika domin an ba shi mukamin ministan harkokin wajen Jamus, inda a nan ma ya fito da matsayin gwamnatin Jamus a fagen siyasar duniya, kamar jawabin da ya yi a New York a ranar 12 ga watan Oktoba na 2010 bayan an zabi Jamus a Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya.

Ya ce: "Muna goyon bayan aiki na zahiri a Kwamitin Sulhu za mu zama kawayen dukkan membobin Majalisar Dinkin Duniya. Muna farin cikin cewa yanzu za mu karfafa aikin da muke yi na tabbatar da zaman lafiya da tsaro da kare muhalli da raya kasa da kuma kawo karshen tserereniyar mallakar makaman nukiliya a duniya."

A lokaci da take bayyana yadda ta samu labarin rasuwar Westerwelle shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi:

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Getty Images/C. Court

"Na kadu da jin labarin mutuwarsa. Ina mika ta'aziyata ga iyalan Guido Westerwelle. Kazalika a wannan lokacin kamar sauran 'yan kasa ina tunawa da irin nasarorin da Guido Westerwelle ya samu a fagen siyasa, wanda tun yana matashi ya dare mukamin shugaban jam'iyyar FDP da kuma irin rawar gani da ya taka a matsayin ministan harkokin wajen Jamus."

An dai haifi Guido Westerwelle ne a ranar 27 ga watan Disamban 1961 a garin Bad Honnef da ke kusa da birnin Bonn, iyayensa lauyoyi ne. Allah Ya yi masa baiwa ta iya magana, ga shi kuma da dattako, kuma shi ne wani jigon dan siyasar Jamus da ya fito fili ya bayyana cewa shi dan luwadi ne.