Guguwar neman sauyi a Kwango | Siyasa | DW | 22.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Guguwar neman sauyi a Kwango

A Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango, al'umma na ci gaba da nuna rashin amincewarsu da yunkurin da gwamnati ke shirin yi na canja dokar da ta shafi zabe a kasar.

Masu zanga-zanga a birnin Kinshasa ba su da niyar gudu ko kuma ja da baya a yunkuri da suka yi na kare demokaradiya a kasarsu. Sun shafe kwanaki suna fantsama a kan titunan babban birnin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango don gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Guguwar neman sauyin ba ta tsaya a nan ba, ta karada a wasu birane irin Bukavu da Goma a arewaci da kuma Kivu a kudanci inda ba a bar mazaunansu a baya ba wajen nuna rashin amincewa da take-taken Shugaba Kabila na gudanar da mulkin sai madi ka ture. Dukkaninsu na nuna turjiya da daftarin doka da ake niyar bita tare da albarkanta a majalisar dokoki kan dokar da ta shafi tsarin zabe a kasar. Lamarin da masu adawa da wannan yunkuri suka ce ba za ta sabu ba. Saboda haka ne suke ta takun saka da jami'an tsaron kasar, wanda ya kai ga mutuwar mutane 11, yayin aka kame kusan 300.

Babbar matsalar da ake fuskanta a halin yanzu shi ne rarrabuwar kawuna tsakanin 'yan adawa na Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango. Jam'iyyun adawa sama da 12 ake da su a wannan kasa. Sannan ma madugunsu Etienne Tshisekedi ya na kasar Beljium yanzu haka inda yake fama da rashin lafiya. Saboda haka ne Philippe Biyoya malamin kimiyar siyasa a jami'ar Kinshasa ya ce da kamar wuya su kai ga hambarar da gwamnatin kabila.

"'Yan adawa na kasar Kwango ba su da wani karfin fada a ji, illa dogara kan kasashen waje kamar yadda ya saba. Ba su da wata kwakkwarar dabara ta kashin kansu, da zata basu damar samun hadin kan talakawan kasar."

Shi dai shugaba Joseph Desiré kabila wanda ya shafe shekaru 14 a kan kujerar mulki, ba shi da hurumin sake tsayawa takara a zaben shekar ta 2016 bisa ga kundin tsarin mulkin wannan kasa. Sai dai kuma 'yan adawa na zarginsa da son yin amfani da sabuwar dokar zabe wajen tsawaita wa'adinsa na mulki. Alalhakika dai daftarin dokar ya tanadi yin sabuwar rejista ga daukacin 'yan kasar Kwango Demokaradiya kafin gudanar da sabon zabe na shugaban kasa da kuma na 'yan majalisa. Lamarin da zai iya daukan lokaci kafin a aiwatar da shi, tare da ba wa kabila damar yin tazarce a fakaice.

Da ma dai wasu sassa na Jamhuriyar Demokaradiya Kwango na fama da wasu rikicen tawaye. Wannan halin ne ma ya sa majalisar Dinkin Duniya turawa a dakaru dubu 20 don kiyaye zaman lafiya a wadannan yankuna. Wakilin manzon musamman na sakataren MDD a Kwango Abdallah Wafy ya yi kira da a mutunta kundin tsarin mulkin kasar.

"Mun damu ainun da tashen-tashen hankula da suka barke sakamakon daftarin kwaskware tsarin zabe da aka shigar majalisar dokokin Kwango. Muna ganin cewa zai fi dacewa a ce shirye-shiryen zabe da aka fara sun samun amincewar kowa da kowa, kuma a mutunta kundin tsarin mulki da kuma 'yancin kowa da kowa."

Sauti da bidiyo akan labarin