Guguwar Irma ta halaka mutane a Holland | Labarai | DW | 08.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Guguwar Irma ta halaka mutane a Holland

Guguwar ta afkawa yankin tsibirin Caribbean na Saint Martin inda ta halaka mutane baya ga wadanda suka samu rauni, wasu raunin nasu ya yi muni sosai.

Bala'in guguwar Irma ta halaka mutane biyu a kasar Holland baya ga wasu 43 da ta raunata, hakan ya biyo bayan afka wa yankin tsibirin Caribbean na Saint Martin, kamar yadda mahukunta akasar suka bayyana a wannan rana ta Juma'a.

Ministan harkokin cikin gida Ronald Plasterk ya bayyana cewa ba shi da cikakken bayani kan su wane ne lamarin ya ritsa da su, sai dai ya tabbatarwa 'yan jarida cewa mutane biyu sun rasu yayin da 43 suka samu raunika, uku daga cikinsu lamarin ya yi muni sosai a cewar ministan.