Gudun hijira daga Sudan ta Kudu zuwa Sudan | Labarai | DW | 15.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gudun hijira daga Sudan ta Kudu zuwa Sudan

Daruruwan mata da yara kanana da suka kaurace wa matsugunansu a Sudan ta kudu sakamakon tashin hankali sun isa birnin Khartum na Sudan domin neman mafaka.

Sudan ta Kudu wacce ta samu 'yancin kanta shekaru byiar da suka gabata ta na fama da baraka tsakanin shugabanninta kan harkokin mulki, lamarin da ya haddasa yakin basasa tare salwantar da rayukan dubban mutane a cikin shekaru biyu na baya-bayannan.

Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da gargadi game da yiwuwar barkewar sabon fada tsakanin bangaren Salva Kiir da Riek Machar duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma. Tuni ma hukumomin kasa da kasa suka fara kwashe ma'aikatansu daga Juba bayan da rikici karshen makon ya yi awon gaba da wasu jami'an agaji na kasa da kasa.

Wannan tashin hankali da ake fama da shi a Sudan ta Kudu ne zai mamaye ajandar taron koli na kungiyar kasashen Afirka ta AU wanda Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon zai halarta a kasar Ruwanda.