Gudun ambaliya a Indonesiya | Labarai | DW | 24.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gudun ambaliya a Indonesiya

Sama da mutane 120,000 ambaliyar ruwa ta tilastawa barin muhallansu a lardin Aceh kamar yadda jami'ai suka bayyana a kasar ta Indonesiya.

Wannan ambaliya dai na zuwa ne adaidai lokacin da lardin ke shirin bukin tunawa da ambaliyar ruwar tsunami shekaru goma da suka gabata , bikin da za a yi a ranar 26 ga watan Disamba.

A cewar Sutopo Nugroho mai magana da yawun maaikatar da ke lura da al'amuran da suka shafi afkuwar bala'oi a kasar yankuna bakwai ne dai a lardin na Aceh ambaliyar ta mamaye tun daga ranar Lahadi biyo bayan ruwan sama mai karfin gaske da aka yi a yankin.

Mutanen dai da aka tabbatar da rasuwarsu a Indonesiya sakamakon ambaliyar ruwan ta Tsumani a ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 2004 sun haura mutane 130,000.