1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gubar dalma ta halaka yara a Najeriya

Yusuf BalaMay 14, 2015

Idan ba a manta ba a shekarar 2010 ne irin wannan gubar dalma ta halaka yara 400 yayin da wasu kimanin 2000 abin ya shafa a jihar Zamfara.

https://p.dw.com/p/1FPrp
Gold waschen in Bagega Zamfara Nigeria
Hoto: Aminu Abdullahi Abubakar

Gubar darma ta hallaka yara kanana 28 a jihar Niger arewa ta tsakiyar Najeriya a cewar gwamnatin wannan jiha cikin rasa rayuka na darurwan mutane da ake samu a kasar a shekarun baya-bayan nan.

Tun daga ranar 12 ga watan Mayu na shekarar nan ta 2015, a cewar Fidelis Nwankwo ministan kasa a ma'aikatar lafiya ta Najeriyar, kuma cikin mutane 65 da suka kamu da cuta saboda gubar ta darma an samu yara 28 da suka rasu.

A jawabin ministan ga manema labarai a Abuja fadar gwamnatin Najeriya gubar darmar da aka samu a cikin jinin mamatan ta wuce kima mafi kankanta da ake samu a binciken kasa da kasa.

Minista Nwankwo ya ce lamarin na faruwa ne yadda ake ci gaba da samun wurare sabbi da mutane ke zuwa hakar zinare da suke dauka zuwa gidaje inda suke sarrafawa ba bisa ka'ida ba. Suma dai dabbobi abin ya shafesu.

Idan ba a manta ba a shekarar 2010 ne irin wannan gubar darma ta halaka yara 400 yayin da wasu kimanin 2000 abin ya shafa a jihar Zamfara arewa maso yammacin Najeriya, jihar kuma da ke hada iyaka da jihar ta Niger daga arewaci. A bin da kungiyar likitoci marasa shinge ta MSF ta bayyana da cewa shi ne mafi muni a tarihin illar da gubar ta darmar ke yi.