Goyon baya ga jam′iyar Ennadah a kasar Tunisiya | Labarai | DW | 10.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Goyon baya ga jam'iyar Ennadah a kasar Tunisiya

A wani abunda ke zaman martani ga zanga zangar da masu adawa da gwamnatin Tunisiya suka yi, bayan kisan madugun adawa, magoya bayan gwamnati sun gudanar da jerin gwano.

A wannan Asabar da ta gabata ne, dubun dubatan magoya bayan jam'iyar Ennadah a kasar Tunisiya, dake kiran kanta jam'iyar 'yan uwa musulmi ne suka fito a kan titunan kasar domin nuna goyon bayan su ga hukumomin kasar bayan zanga zangar da aka share a kalla kwanaki biyar ana gudanarwa a kasar biyo bayan kisan madugun 'yan adawan kasar Chokri Belaid dake sukar manufofin gwamnatin. To saidai a yayin wannan jerin gwanon na lumana an ji magoya bayan jam'iyar ta 'yan uwa musulmi na kira da praministan kasar Hamdi Jebali, da shi sauka daga kan iko a wani matakin martani bayan da ya kira da a kafa gwamnatin hadaka domin kwantar da hankullan masu borai . To dama dai tun can farko babu jittuwa tsakanin shugaban kasar Marzuki da praministansa Jebali dake zaman doya da manja tun bayan hukuncin gaba gadinsa da praminisatan ya dauka na tusa keyar tsohon praministan Kaddafi a kasar Libiya ba tare da sanin shugaban kasar ba. Yanzu haka dai tun bayan kifar da gwamnatin Ben Ali,har ya zuwa yanzu kasar bata zauna da kafafuwanta ba inda ake yawan samun hargitsi a tsakanin al'umar kasar da kuma magabatan.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal