Gomman 'yan kabilar Rohingya sun mutu a Myanmar
August 10, 2024Talla
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, harin jirgi maras matuki ya rutsa da iyalai da dama da ke kokarin tsallaka iyakar Myanmar zuwa makwafciyarta Bangladesh. Wasu alkalumma da ba a tabbatar da su a hukumance ba sun ce kimanin mutane 200 ne suka gamu da ajalinsu a harin.
Wannan na kasancewa hari mafi muni kan fararen hula da ke jihar Rakhine, cikin makwannin da aka kwashe ana gwabza kazamin fada tsakanin dakarun Myanmar da kuma 'yan tawaye. Wasu da lamarin ya auku a gaban idonsu sun dora alhakin kai harin da mayakan Arakan, zargin da kungiyar ta musanta. Sai dai dakarun Myanmar da 'yan tawayen na ci gaba da zargin juna da alhakin kai harin.