Gombe: Tallafawa marasa lafiya | Himma dai Matasa | DW | 13.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Gombe: Tallafawa marasa lafiya

Wani matashi ya kirikiri wasu motoci masu taya uku na daukar marasa lafiya guda goma sha daya domin samun saukin daukar mata masu ciki daga yankuna karkara inda motoci ba iya shiga.

Shi dai Injiniya Garba Musa Gwani wanda sana'ar sa kere-kere ne na zamani ya ce ya yi tunanin kera wadan nan motoci masu tayu uku ne saboda rage samun matsalar sufurin marasa lafiya da yanunan karkara da motoci ba sa iya shiga.

Wannan matsala tafi shafar mata masu ciki inda wani lokaci akan rasa abin hawa da za a kai su cibiyoyin lafiya domin haihuwa sai dai ala tilas su haihu a gida ko kuma akan hanyar su ta tafiya da kafa don zuwa asibiti. Wannan matashi dai ya kirikiri motocin daukar marassa lafiya da kayan Keke NAPEP tare da sanya gadaje da cikakkun na'urori na kula da marassa lafiya ko mata masu ciki domin ba su agajin gaggawa kafin a aki su asibiti kamar yadda Injiniya musa gwani ya shida min.

Tuni dai kwalliya ta fara biyan kudin sabulu don kuwa yankunan da aka raba wadan nan motocin masu tayu uku sun fara ganin alfanun su inda ake amfani da su wajen kai marassa lafiya asibiti mafi kusa da su.