1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta yi barna a filin jirgin Tripoli

August 25, 2014

JIragen yaki na ci gaba da kai hare-hare a Tripoli bayan da fadace-fadace suka lalata wani bangare na filin tashi da saukan jiragen sama na babban birnin kasar ta Libiya.

https://p.dw.com/p/1D08k
Hoto: Reuters

Gobara ta lakume wani sashe na filin jirgin saman birnin Tripoli na kasar Libiya, bayan da mayakan Misrata suka samu kwaceshi daga mayakan Zenten. Sai dai ba'a san ko su wanene suka sanya wannan wuta ba, inda bangarorin dake fafatawa da juna, suka yi ta zargin junansu a wasu sakwanni da suka yi ta aikawa ta shafin internet.

Da asubahin yau din nan (25.08.2014) ma wasu jiragen yaki da ba'a tantance ba, sun kai hare-hare a wasu wurare da dama na birnin Tripoli, inda al'umomin wannan birni, suka yi ta jin karan fashewar wasu ababuwa.

Sa dai kawo yanzu babu wani cikeken labari kan halin da ake cikin a wannan kasa dake fuskantar rikici mafi muni tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Mouammar Kadhafi a shekarar 2011. Wannan gobarar dai ta haddasa barna mai yawa a filin jirgin na Tripoli inda ta lalata jirage, da ma gidaje masu yawa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita Mouhamadou Awal Balarabe