Gobara ta tashi a majalisar dokokin Kamarun | Labarai | DW | 17.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta tashi a majalisar dokokin Kamarun

Wata gobara da ba a kai ga gano musabbabinta ba ta lashe wani bangare na majalisar dokokin kasar Kamaru da ke Yaounde babban birnin kasar a cikin daren jiya Alhamis.

Gobarar dai ta tashi ne daga bangaran ofishin ma'aikatar majalisar, sai dai kuma ana ganin zauran mahawarar baya daga cikin wanda hutar ta kona wadda sai ya zuwa asubahin wannan Juma'a ne ma aka kai ga kashe wutar ga baki daya. An yi ta ganin balbalin wuta na tashi a hawa na uku da kuma na hudu na ginan majalisar kamar yadda sheidun gani da ido suka sanar, da kuma gidan radiyon CRTV ta shafinsa na Twitter. Jami'an tsaro dai sun killace majalisar dokokin inda gobarar ta afku sannan 'yan majalisa da dama na dukannin bangarori tare da shugaban majalisar dokokin Cavaye Yéguié Djibril duk sun isa domin ganewa idanunsu yadda gobarar ta yi.