Gobara ta ritsa da ′yan gudun hijira a Jamus. | Labarai | DW | 10.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta ritsa da 'yan gudun hijira a Jamus.

Mutane 22 ne yanzu haka ke samun jinya a asibiti sakamakon hayakin gobarar da suka shaka a gidan da suke zaune a garin Witzenhausen da ke Hesse.

Deutschland Brand Feuer Feuerwehr Limburg Haus

Mutane 22 da ke zaune a wani gidan 'yan gudun hijirar nan Jamus, sun jikkata sakamakon barkewar gobara da sanyin safiyar wannan Larabar. A cewar mai magana da yawun 'yan sandan da ke jihar Hesse inda nan ne gobarar ta auku, dukkaninsu na samun jinya a asibiti sakamkon hayakin gobarar da suka shaka.

Kawo yanzu dai babu masaniya dangane abun da ya jagoranci gobarar data fara tun cikin daren jiya daga wurin ajiyar kayayyaki dake karkashin ginin, sai dai ana cigaba da gudanar da da bincike.

Rundunar 'yan sanda na Hesse sun shaidar da cewar, jami'an kashe gobara sun cimma gaggauta fitar da mutane 23 dake zaune a gidan 'yan gudun, amma kafin nan 22 daga cikinsu sun jikkata daga hayakin da ya turnukesu.'Yan gudun hijira da ke nan Jamus dai kan fuskanci cin zarafi ta siga daban daban a lokuta da dama.