Gobara ta kashe mutane 36 a Pilipin | Labarai | DW | 02.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta kashe mutane 36 a Pilipin

Wani dan bindinga a Pilipin ya bude wuta da ya haddasa gobara a Otel da wani gidan caca a Manila babban birnin kasar, harin ya yi sanadiyar mutuwar mutane cikin azaban rashin numfashi na tirnikewar hayaki.

Harin ya yi mumunar ta'adi ga dandazon jam'a da ke gudun tsira daga kan beni, jami'an tsaro sun janye bayanin farko da ke alakanta harin da ta'addanci, inda ake hasashen maharin da dan fashi. Amma sun tabbatar da mutuwar maharin sa'o'i kalilan bayan bankawa kansa wuta.

A yanzu dai jami'an tsaro sunce fargaba ta fara lafawa, inda ake ci gaba da daukan tsaurara matakan tsaro, a inda harin ya faru dama sauran harabobin da mutane ke taruwa.