Gobara ta kashe mutane 27 a Potugal | Labarai | DW | 16.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta kashe mutane 27 a Potugal

Wata mahaukaciyar gobara mai karfin gaske ta barke a cikin dokar jejin gabashin kasar Potugal, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 27, inda wasu mutane 51 ke fama da munanan raunuka.

Hukumomin kasar dai sun ce ibtala'in ya shafi kasashe da ke makotaka da Potugal, inda gobarar ta haddasa mutuwar mutane hudu a kasar Spain. Jami'an kashe gobara dai sun ce wutar ta fara ne bayan tirnikewar hayaki a gabashin kasar da ke cike da dokar jeji.

A yanzu dai masu ayyukan ceto na ci gaba da kokarin kashe gobarar, wannan gobara dai ita ce karo na hudu da kasar Potugal ke fuskanta a cikin wannan shekara ciki har da gobarar da ta kashe mutane 64 a watan Yunin da ta gabata.