Gobara ta kashe dalibai a Malesiya | Labarai | DW | 14.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta kashe dalibai a Malesiya

Dalibai 22 tare da malamai biyu ne suka mutu a yayin da mummunar gobara ta tashi a wata makarantar kwana ta Islamiya da maza zalla ke karatu a ciki a tsakiyar Kuala Lampur babban birnin kasar Malesiya.

Mazauna kusa da makaranatar sun ce sun yi ta jin kukan dalibai daga saman bene suna neman agaji, bayan da suka ga hayaki ya tirnike benayen da daliban ke kwana a ciki. Hukumomin agajin gaggawa a kasar sun ce daliban sun galabaita daga shekar bakar hayakin katifu da tsummakarai sakamakon rashin hanyar fita daga harabar makarantar, wannan kuwa ya faru ne biyo bayan yadda aka killace ginin da shinge wanda ya tilasta wa daliban tsalle ta taga daga saman bene.