Gobara ta hallaka mutane 30 a Romaniya | Labarai | DW | 31.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta hallaka mutane 30 a Romaniya

Wutar ta tashi a wani gidan rawa da ke Bucharest fadar gwamnatin Romaniya inda kusan mutane 30 suka hallaka, sannan wasu fiye da 180 suka samu raunika.

Mahukuntan kasar Romaniya sun tabbatar da mutuwar kusan mutane 30 yayin da wasu fiye da 180 suka samu raunika sakamakon gobarar da ta tashi a wani gidan rawa da ke birnin Bucharest fadar gwamnatin kasar. Sannan hukumomin sun ce akwai yuwuwar alkaluman za su karu.

Wutar ta tashi lokacin da ake wata waka da ake amfani da kayayyakin wasan wuta. Tuni aka kaddamar da bincike. Shugaba Klaus Iohanni na kasar ta Romaniya ya nuna takaici kan abin da ya faru.