Gobara ta halaka majinyata Corona a Masar | Labarai | DW | 26.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara ta halaka majinyata Corona a Masar

Mutane bakwai da ke jinyar cutar Corona sun mutu bayan da wuta ta tashi a asibitin da suke karbar jinya a birnin Alkahira na Masar. Sai dai ba a san me ya haddasa gobarar ba tukuna.

Masu fama da cutar Corona akalla bakwai sun mutu a Masar sakamakon tashin gobara a asibitin da ake jinyan marasa lafiya a kusa da babban birnin Alkahira.

Hukumomin sun tabbatar da karin wasu mutane akalla biyar da gobarar ta jikkata, ba a gano musabbabin tashin gobarar a asibitin ba, amma jami'an kashe gobara sun shawo kan matsalar.

A watan Yuni, wasu majinyata sun mutu a wani asibitin shi ma inda gobara ta tashi yayin da wasu da dama suka jikkata.