GMF: Dole kafafen labarai su wanzar da zaman lafiya | Siyasa | DW | 25.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

GMF: Dole kafafen labarai su wanzar da zaman lafiya

Mahalarta taron da DW ta shirya sun yi ammanar cewa kafofin yada labarai na gargajiya da na zamani, za su iya taka rawar gani wajen kawo zaman lafiya a sassa daban-daban na duniya.

Rikici tsakanin kabilu ko kuma addinai, batu ne da ya zama ruwan dare kama a Afirka har ma da wasu kasashen Larabawa. Wannan na daga cikin batutuwan da babban taron karawa juna sani na kafofin yada labarai na duniya da tashar DW ta shirya a nan birnin Bonn ya tattauna a kanshi a rana ta karshe ta wannan taro.

Kwararru masana da suka hada da masu rajin kare hakokin bil-Adama, da masana kimiyar siyasa da kuma sauran wakillan kungiyoyi masu zaman kansu da suka fito daga sassa daban-daban na Afirka, gabas ta tsakiya da kuma nan Turai sun yi bayannai sosai tare da bayar da misalai kan irin rigingimun da aka fuskanta ko ake fuskanta a kasashe musali kamar su Lebanon da Jamhuriyar Afirka ta tsakiya inda rikici tsakanin addinai ko kabilu ya haddasa koma baya mai yawa.

GMF 2015 Digital media, citizen journalism, and whistleblowing

'Yan jarida sun yi musayar yau kan sabuwar hanyar watsa labarai

Shi dai tsarin kafofin yada labarai na gargajiya da na zamani, tsari ne da ya kawo babban ci gaba. Sai dai kuma kafofin sun kasance masu baki biyu, suna kwantar da tarzoma tare da samar da zaman lafiya, ko kuma haifar da tashin hankali, ga misali idan aka dubi yadda 'yan kungiyar IS ko Boko Haram da ke amfani da shafuka na zamani wajen yada bayannan farfaganda. ko da 'yan Pegida a nan Jamus masu fafutukar kyamar yaduwar Muslunci a Turai, su na amfani da shafuka domin yada manufofinsu.

Akayiz Valente wani mai fafutukar kare hakin dan Adam ne a kasar Ruwanda ya tuna baya. Ya ce " Sanin kowa ne ga abubuwan da suka faru a baya a kasata Ruwanda na kashe-kashen gilla ga dubban al'umma wutace wadda ana iya cewa kafofin yada labarai suka kara rura ta, amma kuma a yanzu har abin ya zame babbar matsala ga rayuwar dan Adam, yanzu kuma bayan rikici shi ne muke fatan kafofin yada labarai su karkata akalarsu wajen isar da sakwanni masu kwantar da hankula."

GMF 2015 The human right to freedom of religion in the digital age

'Yan Afirka sun bayar da gudunmawa kan Zaman lafiya a taron GMF

A kasashe da dama 'yan siyasa masu mulki ko neman mulki ne suke amfani da al'umma ta hanyar addinansu ko kabilanci wajen raba kawunansu. Don haka ya kyautu shugabannin addinai su tashi tsaye wajen ganin sun hada kawuann magoya bayansu, yayin da wasu ke ganin cewa ya kyautu a kawo canjin tunani a kawunan al'umma ta yadda amfani da kafofin sadarwa na zamani za su kasance hanyoyi na samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al'umma.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin