Girka ta yi alkawarin biyan bashin da ke kanta | Labarai | DW | 06.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka ta yi alkawarin biyan bashin da ke kanta

Ministan kudin kasar Girka Yanis Varoufakis, ya ce kasarsa za ta biya bashin da ta karba daga asusun bada lamuni na IMF cikin wannan mako.

Ministan kudin na Girka dai ya fadi hakan ne a ganawar da suka yi da shugabar asusun na IMF Christine Lagarde a birnin Washington na kasar Amirka, don tattaunawa kan kiki-kakar bashin da ke gigita kasar ta Girka, kamar yadda ya fito cikin wata sanarwar da IMF din ya fitar.

Mr. Varoufakis dai ya yi kurarin cewar gwamnatin Girka ta tsara ingantattun matakan bunkasa harkokinta a yanzu.

Da wannan matsayin da kasar ta bayyana a yanzu dai, ana sa ran za ta biya asusun na IMF Euro miliyan 450, wani kashin kenan, a ranar Alhamis.

Girkar dai na ta tattaunawa da kasashen da ta ranto kudade daga gare su, hanyoyin da za ta bunkasa tattalin arzikinta, don ta ci gaba da samun kudade.