Girka ta cimma matsaya kan batun bashi | Labarai | DW | 14.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka ta cimma matsaya kan batun bashi

'Yan majalisun dokokin kasar Girka sun amince da matakan ceto tattalin arzikin kasar karo na uku da kasashe masu bayar da bashi suka gindaya musu.

Zauren majalisar dokokin kasar Girka

Zauren majalisar dokokin kasar Girka

Rashin amincewar wasu mambobin jam'iyya mai mulki ta Syriza ne ya hana a samu nasarar kaiwa ga matsaya a muhawarar da suka kwashe tsahon daren jiya suna tafkawa. 'Yan majalisar na Girka dai sun kai ga cimma matsaya sa'oi kalilan gabanin taron ministocin kudi na kasashen da ke amfani da kudin Euro wato eurozone da za su gudanar a birnin Brussels na kasar Beljiyam domin yin nazarin yarjejeniyar. Firaministan kasar ta Girka Alexis Tsipras wanda ke cikin tsaka mai wuya bisa matsin lambar jam'iyyarsa da kuma kasashen da ke bayar da bashin, ya ce kin ya zamo wajibi a amince da sharuddan da aka gindaya musu kafin a basu bashin, domin kuwa kin amincewar ka iya sake jefa kasar cikin rudani da tashin hankali.