Girgizar kasa ta kashe mutane tara a Japan | Labarai | DW | 15.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgizar kasa ta kashe mutane tara a Japan

Jami'an agaji na cigaba da aikin ceton mutanen da suka makale a tsakanin dubban gidajen da suka ruguje, sakamakon mummunar girgizar kasar.

A kalla mutane tara ne suka rasa rayukansu sakamakon wata mummunar girgizar kasa data ritsa da tsibirin Kyushu da ke kudancin kasar Japan a daren wannan Jumma'ar.

Rahotanni kafofin yada labarun kasar na nuni da cewar wasu mutane 760 suka jikkata, 44 daga cikinsu kuwa munana.

Sama da mutane 4000 da ke zaune a wannan tsibiri ne dai suka tsere daga gidajensu, saboda tsoron abun da zai iya biyo bayan girgizar kasar mai karfin maki 6.5.