1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Mutane 37 girgizar kasa ta hallaka a Pakistan

Suleiman Babayo
September 25, 2019

Mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa a Pakistan sun kai 37 yayin da wasu daruruwa suka samu raunika.

https://p.dw.com/p/3QESP
Pakistan Erdbeben
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Naveed

Kusan mutane 40 aka tabbatar sun mutu sakamakon girgizar kasa da aka samu a kasar Pakistan. Girgizar kasar mai karfin maki 5,8 da kuma janyo kimanin mutane 500 sun samu raunika.

An samu girgizar kasar a yankin Kashmir da ke hannun Pakistan inda lamarin ya shafi birnin Mirpur da kauyukan da ke kewaye da birnin.

Ana tababa kan mallakan yankin na Kashmir tsakanin kasashen Indiya da Pakistan kuma yanzu haka akwai layin da ya tsaga tsakanin bangarorin biyu kuma ana samu tashe-tashen hankula lokaci-zuwa lokaci.