1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Girgizar kasa a Indonesiya

April 12, 2019

Indonesiya ta sake fuskantar wani sabon ibtila'in girgizar kasa a tsibirin da aka sami makamancinta a bara. Lamarin ya harzuka mazauna tsibirin Sulawesi.

https://p.dw.com/p/3Ggl0
[No title]

Hukumomin kasar Indonesiya sun kawar da yiwuwar samun igiyar ruwan tsunami a kasar, bayan afkuwar girgizar kasa a tsibirin Sulawesi a ranar Juma'a.

Lamarin da ya faru da misalin karfe 11:40 agogon GMT, ya kai zurfin kilomita 10 a karkashin kasa, abin kuma da ya harzuka jama'a.

Babu dai wani rahoton tsananin barnar da girgizar kasar ta haddasa ya zuwa yanzu, sai dai an gargadi mazauna da su yi nesa da yankin.

Akalla dai mutum dubu 4,300 suka salwanta a bara a yankin Palu da ke a tsibirin na Sulawesi, sakamakon girgizar kasar da ta hadu da ibtila'in igiyar ruwan tsunamin.