Girgizar ƙasa a Iran | Labarai | DW | 31.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girgizar ƙasa a Iran

`Yan makaranta a nahiyar Afirka

`Yan makaranta a nahiyar Afirka

A ƙasar Iran an bada rahoton aukuwar girgizar ƙasa mai ƙarfi da ta karaɗe yammacin ƙasar da sanyin safiyar yau. Mutane 28 sun riga mu gidan gaskiya yayin da kuma wasu kimanin 700 suka sami raunuka. Kamfanin dillancin labarai na ƙasar Iran ya ruwaito cewa gigizar ƙasar wadda ke da awo shida a maáunin ritchter ta auku ne a rukunin masnaántu na wasu yankuna biyu a yammacin ƙasar. Maáikatan ceto sun isa yankin domin taimakawa waɗanda girgizar kasar ta rutsa da su. A sheakarar 2003 gigizar ƙasar da ta auku a lardin Bam a kudancin Iran ta hallaka mutane kimanin 31,000.