Ginshiken Turai na Bai-daya na Mahangar Harsuna | Einstufung | DW | 13.06.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Einstufung

Ginshiken Turai na Bai-daya na Mahangar Harsuna

Ginshiken Turai yana samar da hadaddiyar hanya don koyon harshe a a fadin kasashen Turai.A cikin tabbatattun matakai shida, yana bayyana kwarewar da mai koyo ke da ita a kowane mataki a hanyar koyo.

Mataki na A1 - Farawa
Koyi yadda za ka iya fadar muhimmai, kamar inda ka ke zaune da kuma menene abubuwan nishadin ka.

Mataki na A2 - Sadar da muhimman bayanai
Za ka iya yin magana game da muhimman darussa kuma ka bayyana bukatunka - kamar lokacin da ka ke siyayya.

Mataki na B1 - Gudanar da halayen yau da kullum

Yayin da ka ke kewaya kasar Jamus, za ka iya tafiyar da yawancin halayen da ke sami kanka ciki. Za ka iya yin magana game da abubuwan da ka gani sannan ka bayyana ra'ayinka a fili.

Mataki na B2 - Kasance mai iya bayani
Za ka iya sadarwa a kowane yanayi ba tare da tangarda ba - koda kuwa a dogayen hirarraki ne tare da 'yan asalin yaren. Za ka iya bibiyar rubutu mai tsauri da muhawarori sannan ka bayyana ra'ayinka akan boyayyun darussa.

Mataki na C1 - Yi magana ba fargaba
Ba sai ka yi binciken kalmomi ba inda za ka iya yin magana da harshen Jamusanci hankali kwance ba tare da shan wahala ba a cikin kowane hali. Za ka fahimci bayanai masu tsawo, da tsauri.

Mataki na C2 - Fadi bukatu
Za ka fahimci duk abin da ka karanta kuma ka ji kuma za ka iya sadarwa a kowane yanayi ba tare da tangarda ba, kana mai isar da cikakkun bayanai.