1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunƙurin Isra'ila na gina matsugunan Yahudawa

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 30, 2015

Isara'ila ta sanar da cewa ta bayar da umurnin gina ɗaruruwan matsugunan Yahudawa nan take a Gabar Yamma da Kogin Jodan da kuma gabashin birnin Kudus.

https://p.dw.com/p/1G7FE
Sababbin matsugunan Yahudawa a Gabar Yamma da Kogin Jodan.
Sababbin matsugunan Yahudawa a Gabar Yamma da Kogin Jodan.Hoto: Reuters/B. Ratner

Isra'ila dai ta ƙwace iko da waɗannan yankuna ne tun a shekara ta 1967 yayin yakin Gabas ta Tsakiya. Har kawo yanzu dai Falasdinawa na yin ikirarin cewar wannan yanki mallakinsu ne da za su kafa ƙasar kansu a wajen. Tuni dai Amirka ta nuna matukar damuwarta a kan wannan sabon kudiri na Isra'ila wanda ka iya fuskantar tirjiya daga al'ummomin ƙasa da ƙasa. Dama Isra'ila ta jima ta na barazanar gina sababbin matsugunan Yahudawa a wannan yanki da suke taƙaddama a kansa ita da Falasɗinu wanda kuma al'umomin ƙasa da ƙasa ke nuna damuwarsu da kuma adawarsu a kan yunƙurin nata wanda suke cewar ya na iya ƙara ta'azzara rikicin da ke takanin Isra'ilan da Falasɗinu.