Gidauniyar yaƙi da cutar Aids ta PEPFAR a Amurka. | Siyasa | DW | 06.05.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gidauniyar yaƙi da cutar Aids ta PEPFAR a Amurka.

Gwamnatin Amurka ta lashi takobin cigaba da yaƙi da cutar Aids mai karya garkuwar jiki a Duniya

default

Shugaba Barack Obama na Amurka ya nuna manufarsa na cigaba da gudanar da gagarumin shirin nan na yaki da cutar AIDs, wadda tsohuwar gwamnatin data gabata ta kaddamar, domin tallafawa kasashe masu tasowa yaki da cutar da kuma samar da magunguna.

Wannan shiri da ake kira PEPFAR a takaice, na ɗaya daga cikin shirye-shiryen da tsohuwar gwamnatin shugaba George W Bush ta samu nasara akansa musamman a kasashen nahiyar Afrika.

A karkashin wannan shiri dai an ware kimanin dalan Amurka biliyan 48, wanda ke nufin tabbatar dacewar dukannin kasashen dake nahiyar Afrika masu fama da cutar HIV sun samu magunguna tare da dorewwarsa.

Wannan shiri da gwamnatin Amurkan ta kaddamar dai na taimakawa wajen ilimantar da waɗanda suka kamu da kwayoyi HIV, wajen kulawa da kawunansu da kuma matakan da zasu dauka.

George W. Bush

Tsohon shugaban Amurka Bush

A yanzu hakan shugaba Barack Obama ya naɗa Dr Erick Goosby, Farfesan magunguna kuma tsohon mai yaki da cutar Aids a matsayin jagoran wannan shiri.

Kungiyoyi masu zaman kansu da masana fannin harkokin kimiyya dai, su na da kyakkyawan fata a akan Dr Goosby mai shekaru 56 da haihuwa, musamman saboda irin fafutukarsa a wannan fanni da ma irin rawa da ya taka a shekarun da suka gabata wajen yaki da cutar ta Aids.

Sai dai masana ilimin kimiyya da kwararru sun soki manufofin shirin na PEPFAR ta ɓangaren hanyar da za a iya samun kariya. Stephen Lewis masanin kimiyya ne a Kanada, kuma tsohon wakilin Kofi Annan akan yaƙi da cutar Aids a Afrika..

Yace "Ɓangaren shirin PEPFAR dake da nufin samar da kariya, ya mayar da hankali ne kacokan kan kauracewa jima'i, ba tare da nuna muhimmancin amfani da hular kariya ba, wanda hakan ya haifar da illoli, musamman tsakanin iyalai, wanda a ganina wannan tsari bashi da ma'ana"


Manufofin shirin PEPFAR na kariya dai a hukumance sune, ƙauracewa jima'i, mutunta juna, tare da amfani da kwaroron roba.

100 Tage Obama im Amt englisch

Shugaba Obama na Amurka

Ana sa ran Dr Goosby dai zai taka muhimmiyar rawa a gwamnati mai ci a yanzu a Amurka, musamman dangane da kwarewarsa a bangaren yaki da cutar Aids da samarda da magunguna aikin daya ɗauki tsawon shekaru 25 yana gudanarwa.

A tsawon wannan lokaci ya taimakawa ƙasashe kamar China da Afrika da kudu da Rwanda, a kokarinsu na yaƙi da cutar Aids mai karya garkuwan jiki.

Masana sun bayyana Farfesan a matsayin mutum guda take da damar amfani da karagar mulkin Obama wajen neman karin tallafin kuɗaɗe domin yaƙi da cutar Aids a duniya baki ɗaya.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Ahmed Tijani Lawal