1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gidan fursuna na yara cikin matsaloli

June 13, 2019

Dubban yara ne masu kananan shekaru ake tsare da su a cikin gidajen kurkuku kuma suna daukar tsawon lokaci suna jiran shari'a.

https://p.dw.com/p/3KNrI
Justiz Liberia
Wannan wani tsohon hoto ne na wani gidan fursuna a Afirka da muka yi amfani da shiHoto: Meredith Safer

A wani gidan yarin gyara halinka da ke Jihar Ogun a kudancin Najeriya yawancin yaran da ke cikin wannan gidan yarin na da shekaru 14. Wannan gidan yarin ne na gyara halinka na yara ko matasa da suka fara bijire wa tarbiyar kwarai. Kungiyoyin masu zaman kansu a Najeriya sun yi tsayin daka kan shirin yunkurin gwamnati na samar da shirin inganta rayuwar yaran da ke zama a irin wannan gida bayan zaman gyara halinka. Wani matashi da ke tsare a gidan ya ce ya tsinci kansa a gidan yarin sama da shekara guda saboda sayar da kwaya. Gidan kurkukun kuma na fama da matsalar rashin kayan aiki sakamakon yada gwamnatin ba ta ba da kulawa kamar yada ya dace.