Gidan tarihi na neman zama tarihi a Nijar | Zamantakewa | DW | 25.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Gidan tarihi na neman zama tarihi a Nijar

A Jamhuriyar Nijar babban gidan tarihin nan mai dadadden tarihi wato Musee nationale ne ya fada a cikin wani garari sakamakon kawanyar matsaloli na ajiyar namun daji.

Afika hungriger Löwe

Zaki sarkin dawa a gidajen ajiyar namun daji a Afirka

A shekarun 1958 ne dai hukumomin kolin kasar hadin gwiwa da Turawan mulkin mallaka suka assasa dandalin na Musee nationale a matsayin bigiren da zai ajiye kayan tarihi na al'adun kabilu daban daban na Afirka musamman ma na Nijar da ma tattara wasu namomin daji da jama'a ke yiwa tururuwa daga kusurwa da lungunan kasar har ma da kasashen waje don kashe kwarkwatar idanunsu.

Ko da yake Allah ya albarkaci Nijar da samun wuraren kallon namun daji har kusan guda 6, babban gidan kallon da ajiye kayan tarihi na musee na a matsayin irinsa na farko da kowa yake sha'awa wanda hatta ma makada da mawakan wancan lokaci suka yiwa guda, sai dai a yanzu batun ba haka yake ba inda matsalolin da gidan ke fuskanta a 'yan shekarun baya bayan nan ke neman su gagari kundila.
Malam Ibrahim Moussa Abdoul aziz daya ne daga cikin ma'aikatan na gidan kallon na Nijar:

Migranten in Agadez

Yanayin gine-ginen tarihi a Agadez

"Matsaloli ne sosai duk abincin da dabbobin nan ke ci nada tsada sosai akwai wasu tsuntsaye abinci da suke ci ya yi tsada, buhun yafi jika hamsin, dorina biyu garemu kowane na cin fiye da kilo 150 ga kuma zakuna da muke da su inda suka kai bakwai kuma duk nama suke ci hakan kuma ruwan da muke biya a wata yakai miliyan uku."


Wata ziyarar da wakilin DW a birnin Yamai Abdoulaye Mammane Amadou ya kai a gidan kallon ya ga yadda matsalolin suke a bayyane inda ko baya ga raguwar wasu namun dajin da aka san gidan kallon da shi a wancan lokaci, wasu daga namun dajin su kan kasance a cikin halin tagayyara, irin tururuwar da ake gani a da don zuwa kallon gidan kuma ta ragu, to amma sai dai a gefe daya ya hangi karin wasu dakunan tarihi kamar na karafen uranium da na man fetur baya ga dakin ajiye kayan al'adu.


Bildergalerie Nashörner

Mugundawa a gidan kallon namun daji

Ga Malam Audu wani dan shekaru kimanin 60 da ya san gidan kallon yau sama da shekaru 36 sakaci da mahukumta sukayi wa gidan tarihin da kallon namun daji shi ne ya haifarda duk wannan matsalar:

"An rage abu da yawa an bar abubuwa da yawa sun tafi da komai akwai ga shi nan ma an jagwalgwala jimina."

Sai dai ra'ayi ya banbanta tsakanin malam Audu da mai jagorar baki a wannan gida:"Domin kuwa duk wata tabarbarewa da gidan ya shiga yana da nasaba ne da wasu dalilai na mahukunta, a ce yanzu museee na son ta samu wata dabba sai ta rubuta wa ministoci wajan uku, hakan abin zai dauki lokaci mai tsawo kwarai." Rahotanni dai na cewar hatta da kasafin kudin da ake warewa gidan a shekara basu taka kara suka karya ba.