1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Zaben fidda gwani na Jam'iyyar NPP

Rahmatu Abubakar-Mahmud
November 3, 2023

'Yan takara hudu ke fafatawa a zaben fidda gwani na Jam'iyyar New Patriotic Party (NPP) ta Ghana domin zabar wanda zai yi wa Jam'iyyar takarar shugaban kasa a zaben 2024.

https://p.dw.com/p/4YNiQ
Zaben Ghana l Wata mai goyon bayan Jam'iyyar NPP a birnin Accra
Zaben Ghana l Wata mai goyon bayan Jam'iyyar NPP a birnin AccraHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

 A wannan zaben fidda gwanin wakilan jam'iyyar sama da 200,000 daga sassa daban-daban na Ghana za su kada kuri'unsu domin zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NPP kuma wanda zai jagoranci jam'iyyar a zaben 2024. Za a gudanar da zaben ne a mazabu daban-daban na dukkan yankuna 16 na kasar Ghana. Wakilai 436 ne za su kada kuri'a a babban ofishin jam'iyyar da ke Asylum Down, Accra. yankin Ashanti, wakilai 34,987 za su kada kuri'a, yayin da wakilai 4,204 za su kada kuri'a a yankin Ahafo. Wakilai 39,134, ne za su kada kuri'a a yankin Greater Accra. Yankin Volta kuma na da adadin wakilai 11,995

Ghana: Zaben fidda gwani na 'yan takarar Jam'iyyar NPP
Ghana: Zaben fidda gwani na 'yan takarar Jam'iyyar NPPHoto: Cristina Aledhuela/AFP

Mutane hudu da ke neman takarar shugabancin kasar sun hada da mataimakin shugaban kasa, Dr Mahamudu Bawumia. Dan majalisa mai wakiltar Assin Central Kennedy Agyapong, tsohon dan majalisa mai wakiltar Mampong Francis Addi-Nimoh, da tsohon ministan noma, Dr Owusu Akoto Afriyie. A halin yanzu hankali yafi karkata tsakanin mutane biyu wato mataimakin shugaban kasa, Dr Mahamudu Bawumia da kuma dan majalisa mai wakiltar Assin ta tsakiya Kennedy Agyapong.

Wasu 'yan Jam'iyyar NPP na kasar Ghana a lokacin yakin neman zabe
Wasu 'yan Jam'iyyar NPP na kasar Ghana a lokacin yakin neman zabeHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Ana dai ci gaba da zarge-zarge daga yankin Kennedy Agyapong na dan majalisa mai wakiltar Assin ta tsakiya da kuma mataimakin shugaban kasa Dr Mahamudu Bawumia tare da zargin shi da ba wa Dan majalisa mai wakiltar Assin ta tsakiya kan cin hanci tare da bukatarsa ya janye daga takarar amma jama'a da dama sun musunta zargin. Alhaji Usman mamba ne na jammiyyar kuma lauya a fadar shugaban kasa ya yi tsokaci.

Karin Bayani: Ghana: Yarjejeniyar zaman lafiya kafin zabe

"Babu kanshin gaskiya a wannan zance, domin ita Kanta Ghana yanzu take samun tallafi daga IMF, sai a ce mutun daya zai mika masa cin hanci na wadannan magudan kudade. Hankali ma ba zai dauka ba”

A halin da ake ciki dai an kira taron gaggawa na yan takarar inda aka shimfida masu wasu kaidoji kamar yadda sakataren jammiyyar Justin Koduah Frimpong ya sanar. Daga cikin abubuwan da 'yan takarar suka rataba hannu akai dai, sun hada da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da amincewa da kaddamara ga duk wanda ya fadi a zaben