1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana ta dauki hankalin jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala
March 3, 2017

Batun samar da shirin tallafin raya kasa na EU ga Afirka da yunkurin shugaban kasar Ghana na farfado da tattalin arzkin kasar da kokarin Afirka na shawo tada kayar baya a Mali sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2YbtX
Afrika Ghana - Nana Akufo-Addo übernimmt das Amt des Präsidenten
Hoto: Reuters/L. Gnago

Jaridar Berliner Zeitung ta fara sharhinta ne da taken "Majalisar dokokin Turai ta yi kiran karin taimako ga Afirka", inda ta ce shugaban majalisar dokokin tarayyar Turai Antonio Tajani ya bukaci kasashen na Turai su samar da katafaren shirin tallafin habaka Afirka na tsabar kudi dala biliyan daya, inda ya ce ko dai mu tashi tsaye a yanzu domin taimaka wa nahiyar Afirka ko kuma miliyoyin 'yan Afirka za su kwararo zuwa Turai cikin shekaru 20 masu zuwa.

Jaridar ta ce shugaban na Majalisar dokokin Turai ya ce akwai bukatar kasashen Turai su zuba jari na biliyoyin Euro domin habaka wanzuwar ci gaba da raya kasa Afirka. Jaridar ta Berliner Zeitung ta yi nuni da cewa  nahiyar Turai na bukatar hikima da dabarun tattalin arziki da dipolomasiyya domin cimma wannan manufa.   

Grenzübergang Spanien Marocco afrikanische Migranten überqueren die Grenze in Ceuta
Han yanzu 'yan Afirka na shiga Turai ta barauniyar hanyaHoto: REUTERS/M. Martin

Yunkurin habaka tattalin arzikin Ghana

Jaridar Süddeutsche Zeitung a na ta sharhin mai taken "karsashi na farfado da tattalin arzikin Ghana a yayin da take cika shekaru 60 da samun yancin kai" ta ce sabon shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya yi waiwayen inda ya ce Ghana wadda ta dade tana zama abar koyi ga sauran kasashen Afirka a yanzu ta kasance tana ja da baya. Yace a shekarar 2011 Ghana ta zama a kan gaba fagen tattalin arziki da zaman lafiya.

Jaridar ta ce sai dai abin da ke ci wa 'yan kasar ta Ghana tuwo a kwarya shi ne yadda ake shigar da kayyaki daga kasuwannin Turai zuwa cikin kasar a farashi mai rahusa da ke kashe kasuwannin kayayyaki na cikin gida. Jaridar ta kara da cewa 'yan kasuwar ta Ghana na masu ra'ayin cewa ya kamata a sanya haraji a kan kayayyakin wadanda suka hada da kaji da ake shigarwa a cikin kasar.

Gemeinsame Patrouillie von Rebellen und Soldaten in Mali
Matsalar tsaro bata kau ba a MaliHoto: picture alliance/dpa/B.Ahmed

Matsalar tsrao a Mali da Burkina Faso

Ita kuwa jaridar die Tagesszeitung a na ta sharhin ta maida hankali ne a kan "hare haren da kungiyoyi masu da'awar addini a Mali suke kai wa a kasar Burkina Faso", inda ta ce a kwananan aka kai harin ta'addanci a wasu chaji ofis guda biyu na 'yan sanda a arewacin Burkina Faso. Harin wanda aka kai a kauyukan Baraboule da Tongomayel a gundumar Soum suna kan iyaka ne a kasar Mali.

Kungiyar Ansarul Islam karkashin jagorancin Imam Ibrahim Malam Dicko wadda ta fara bulla a arewacin Mali a shekarar 2012 da kuma ta kai jerin hare hare a Timbuktu ta yi ikararin kai harin.Jaridar ta ce hadin gwiwar kasashen Afirka da taimakon Amirka da kungiyar tarayyar Turai na bakin kokari wajen taimakawa wajen kawo karshen ayyukan ta'adanncin da kuma samar da ci gaba a Afirka .