Ghana: Sarrafa tsoffin tayoyin mota zuwa kujeru na ado | Himma dai Matasa | DW | 05.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Ghana: Sarrafa tsoffin tayoyin mota zuwa kujeru na ado

A lokuta da dama masu motoci a Ghana na zubar da tayoyin da suka gama cin moriyarsu a matsayin shara, amma yanzu wani matashi na sarrafa wadannan tayoyi zuwa kujeru.

A kasar Ghana ana da miliyoyin ababen hawa musamman motoci, kuma kusan rabin wadannan adadin an fi hawansu a Accra babban birnin kasar. A lokuta da dama masu motocin na zubar da tayoyin da suka gama cin moriyarsu a matsayin shara. Kona taya dai na gurbata iska yayin da zubar da su a duk inda aka ga dama ke haddasa dati mai yada cutar zazzabin cizon sauro. Amma yanzu wani dalibi da ke gabanin kammala karatun jami'a ya soma aikin sarrafa tsoffin tayoyi zuwa kujeru na ado.

Shagon Jeffery Yeboah, dalibi ne a jami'ar kasar Ghana da ke a birnin Accra. Shekaru biyu da suka gabata ya soma tunanin sarrafa tsoffin tayoyin mota zuwa kujeru na ado da za a iya amfani da su a gida ko wuraren shakatawa, domin kawar da sharar tayoyi kadai abu ne mai wahalar gaske, amma komai ya ja hankalin matashin har ya yi wannan nazari?

"Hanyar kawar da tsoffin tayoyi, ita ce a sake sarrafa su, don idan ka gama amfani da tayoyin zubar da su ake, ko jibgesu a wani lungu a gida. Ana hakan amma kuma ka samar wa sauro gurbin zama, za su zama matattarar sauro da ke haifar da cutar maleriya, za mu iya mayar da tsofaffin tayoyin dukiya ta hanyar sake sarrafa su.''

Jeffrey Yeboah a bakin aiki a shagonshi da ke birnin Accra na kasar Ghana

Jeffrey Yeboah a bakin aiki a shagonshi da ke birnin Accra na kasar Ghana

Shakka babu, ana samun sharar tsoffin tayoyi a duk sassan kasar, wasu ana jibgesu cikin magudanan ruwa wasu kuwa konasu ake, daga karshe duk ya gurbata iska. Yeboah kuwa bi yake kwararo-kwararo yana tattara tsoffin tayoyin, ya wanke su tsaf kafin ya soma aikin a kansu. Hakika wannan tafiya ta Yeboah na aiki da basira da ya soma kamar wasan yara ya zame masa yanzu sana'a, sai dai tafiya ce da ke tattare da kalubale.

"Sana'a ce mai wahala. Na soma ta tun farkon karatuna a jami'a, sauran dalibai za su yi ta korafi kan cewa na dame su da zubar da ruwan dattin taya ko na tsare musu wurare da tsoffin tayan, 'yan uwa kuwa ba su ma san mai nake yi ba, su dai korafinsu, ta kaka na gagara kammala karatu suna tambayar komai nake yi ne har yanzu a jami'a.''

Hakika Yeboah bai samu goyon baya daga danginsa ba. Ya soma da akalla dala dari biyar da ya kwashi lokaci yana ajiyewa. Akwai lokacin da yake barin karatunsa don ganin ya cimma burinsa. Daya daga cikin abokansa shi ne Samuel Akpo, ya yaba wa Yeboah.

''Yana matukar birge ni, a ce za a iya sarrafa tsoffin taya haka, muna bukatar irinsu, ba makawa wannan abu ne da zai samar da ci gaba sosai.''

Ga dukkan alamu Yeboah dai na da kuzari da kuma kwarin gwiwa kan wannan sana'ar tasa, kuma ma dai ya soma samun karbuwa a kasar. Ana ganin nan ba da jimawa ba kujerun za su zama na ado a duk sassan kasar Ghana da ma kasashe da ke makwabtaka da ita.

Sauti da bidiyo akan labarin