1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 28 na samun jinya a asibiti

Zainab Mohammed Abubakar
March 22, 2019

Rahotanni sun nunar da cewar hatsarin ya auku ne da misalin karfe biyu na daren jiya a gunduwar Bono da ke yankin gabashin kasar, mai tazarar km 430 daga Accra babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3FVN2
Ecuador Busunglück auf Highway zwisschen Quito und La Mana
Hoto: picture-alliance/Zumapress

Kwamandan rundunar 'yan sanda Joseph Antwi Gyawu ya shaidar da cewar, motocin biyu kirar Bus dauke da mutane 50 kowanne sun yi karo da juna, in da nan take daya ya kama da wuta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 60.

Jami'an agajin gaggawa dai sun kasance a wurin da hatsarin ya auku tare da masu kashe gobara domin bada dauki.

 Kwame Arhin da ke zama likita a asibitin gwamnati na garin Kintampo, ya bayyana cewar akwai wasu mutane  28 da suka jikkata, bakwai daga cikinsu na cikin mawuyancin hali na jinya.