1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Bikin gargajiya na Chale Wote a birnin Accra

August 28, 2018

Bikin gargajiya na Chale Wote karo na takwas a kan gudanar da shi a kan tituna, ya samu halartar kwararru a fannin zane-zane da fasahohi.

https://p.dw.com/p/33tri
Ghana Chale Wote Street Art Festival
Hoto: DW/D. Agborli

A kasar Ghana, an gudanar da bikin baje kolin fasahohin zane da hotuna da fina-finai da kayayyakin gargajiya da abinci kala-kala a unguwar Jamestown da ke birnin Accra. Bikin da ke gudana tsawon mako guda a kowace shekara, a wannan shekara shi ne karo na takwas da ake gudanar da shi da zummar bunkasa al'adun gargajiya da harkokin yawon bude ido.

Bikin na samun halarcin 'yan kasa da baki daga ko-ina cikin duniya wadanda ke zuwa kashe kwarkwatar idonsu. Wata mai suna Olivier daga kasar Italiya na daga cikin bakin da suka halarci bikin na bana da ta ce ya burge ta kwarai da gaske.

"Wannan wata kyakkyawar hanya ce ta hade baki da 'yan kasa a cikin shagali. Ko da yake muna da irin wadannan bukukuwa a kasar Italiya amma suna mayar da hankali ne kan abinci da addini."

Matsafa na gargajiya ma ba a barsu a baya ba a bikin na Chale Wote
Matsafa na gargajiya ma ba a barsu a baya ba a bikin na Chale WoteHoto: DW/D. Agborli

Teh Mensah mai fasahar amfani da kwanukan rufin wajen yin kere-kere. Yanzu haka dai Mensah mai fasahar zane da kira ya fara wani aiki na tsabtace muhalli, inda yake tattara ledojin "Pure Water" na harhda kayan alato da su. Yanzu haka kuma ya fara amfani da tsoffin tayoyin mota yana kera kayakin amfani yau da kullum na cikin gida.

Ga Shamsuddeen kuwa bikin na Chale Wote yana cimma burinsa domin a cewarsa ana ba wa 'yan kasa damar baje kolin kayayyakin al'adunsu na gargajiya tare da fasahohi na zane-zane da wakoki da girke-girke da suke da su domin duniya ta sansu.