Gerher Schröder yayi murabus daga mukamin sa na dan majalisar dokoki | Labarai | DW | 23.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gerher Schröder yayi murabus daga mukamin sa na dan majalisar dokoki

Tsofan shugaban gwamnatin Jamus, Geher Schröder yayi murabus daga matsayin sa, na dan majalisar dokoki.

Kakakin fadar Bundestag ya bayyana wannan labari a yau laraba.

Tun ranar litinin da ta wuce Geher Schröder, ya bayyana wa jam´iyar sa ta SPD shawara da ya yanke, ta yin murabus daga kujera sa ta dan Majalisa, bayan ya kada kuri´ar amincewa da Angeller Merkell,ta zama sabuwar shugabar gwamnati.

Shröder, ya yi zama dan majalisa daga 1980 zuwa 1986, da kuma 1998 ,inda a wannan shekara ne, ya hau karagar mulkin gwamnati Jamus.

Kafofin sadarwa na kasar Jamus na bayana cewa bisa dukkan alamu, tsofan shugaban gwamnatin na Jamus na bukatar komawa aikin sa na assuli wato lauya.