1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar cin kofin Turai

Lateefa Mustapha Ja'afar ZMA
June 21, 2021

Ana ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Turai wato Euro 2020 da annobar COVID-19 ta tilasta dage ta a shekarar da ta gabata, inda Italiya ta samu zuwa zagaye na biyu.

https://p.dw.com/p/3vHuZ
Italien Rom | UEFA EURO 2020 | Italien vs Wales | Tor 1:0
Hoto: Alberto Lingria/AFP/Getty Images

Su ma dai kasashen Beljiyam da Neatherlands sun kusa tsira domin dukansu suna saman tebur a rukunin B da C da maki shida-shida. Sai dai kasashen Faransa da Potugal da Jamus a ke a rukunin F, har yanzu ba su san matsayinsu ba, domin kuwa Faransa da ke saman tebur maki hudu ne da ita kacal, abin da ke nuni da cewa maki daya ne tsakninsu da kasashen Jamus da Potugal da dukansu ke da maki uku-uku.

Hakan dai na nuni da cewa duka kasashen uku tilas su kai bantansu a wasan da za su fafata karo na uku kuma na karshe a zagayen farko na gasar. A ranar Laraba mai zuwa ne dai kasar Potugal za ta kece raini da takwararta da Faransa yayin da Jamus za ta fafata da Hangarai.

Ko ma dai ya ake ciki, kasashen na Jamus da potugal da ma ita Faransan na da damar tsallaka wa zagaye na biyu, in har aka yi la'akari da tsarin nan na wanda ya fi taka rawa a mataki na uku a kowanne rukuni na da damar tsallaka wa zuwa zagaye na biyun.

Su kuwa kasashen Turkiyya a rukunin A da Denmak a rukunin B da Macedorniya a rukunin C da Scottland a rukunin D da Poland a rukunin E da kuma Hangarai a rukunin F sun gaza kai bantensu a wannan gasa.