Garkuwa har da malaman kwaleji a Najeriya | Labarai | DW | 31.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garkuwa har da malaman kwaleji a Najeriya

Wannan dai na zuwa ne lokacin da gwamnan Jihar ta Katsina Aminu Bello Masari ya sanya hannu kan wata doka ta kisa ga duk wanda aka kama ya yi garkuwa da mutane a jihar.

Rahotannin da ke fitowa daga arewa maso yammacin Najeriya sun yi nuni da cewa 'yan bundiga sun yi garkuwa da shugaban gamaiyar kungiyoyin fararen hula na jihar Katsina kuma malami a sashen koyar da aikin jarida na kwalejin kimiya da fasaha ta Hassan Usman da ke Katsina Bishir Usman Ruwangodiya. 

Lamarin ya farune lokacin da malamin ya je kai kudin fansar wani malamin makarantar da 'yan bindiga su kai garkuwa da shi kwanki biyu da suka gabata kamar yadda shugaban kungiyar manyan ma'aikatan makarantar Mansur Garba ya yi wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Jargaba karin bayani. 

Wannan dai na zuwa ne lokacin da gwamnan jihar ta Katsina Aminu Bello Masari ya sanya hannu kan wata doka ta kisa ga duk wanda aka kama ya yi garkuwa da mutane a jihar.