Garkuwa da wasu ′yan Faransa a Kamaru | Labarai | DW | 19.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Garkuwa da wasu 'yan Faransa a Kamaru

Wasu da ba'a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da wasu 'yan Faransa masu yawon buɗe ido a Kamaru

Rahotanni sun ce a yankin arewacin kamaru, an yi garkuwa da wani Iyalin Faransawa bakwai a ciki har da ƙananan yara guda huɗu, inda kamfanin dillancin labarun Associated Press ya rawaito cewa wasu jami'ai na zargin ƙungiyar Boko Haram da hannu a ciki.

Kawo yanzu dai babu cikakken bayani kan wannan batu, amma wata majiya da ta ambaci wani jami'in Faransa da ke da dangantaka da ofishin jakadancin Kamaru yace suna kyautata zaton an ɗauke su daga Kamaru ne an shigar da su Najeriya.

To sai dai a waje guda kuma lokacin wani jawabi da yayi a ƙasar Girka, shugaban ƙasar Faransa Francois Hollande ya gargadi 'yan asalin Faransar da ke yankin da su guji nuna kansu.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar